WOULD - MENE NE SHI, YA YA AKE AIKI DA SHI?

Would ɗaya ne daga verb ɗin da ake kira modal verbs ko kuma modals a taƙaice. Would verb ne da ake aiki da shi a gurare mabambanta. Ma'anar da ya ke ɗauka, ta dogara ga sigar da aka yi amfani da shi. Domin akwai hanyoyi da ake aiki da shi a turanci sama da goma ko kuma wani adadi makamancin haka.

Would kaman sauran modals, ba ya canza wa a lokaci mai ci (present continuous), lokaci sabau (present simple) da kuma shuÉ—aÉ—É—en lokaci. Mutane da yawa kan yi tunanin cewa would past particle na will ne, amma ba haka ba ne. Domin É—aya daga cikin amfanonin would shine aiki a matsayin will a shuÉ—aÉ—É—en lokaci. Would verb ne mai zaman kansa, hakama will.

YADDA AKE SARRAFA WOULD

Sarrafa would ya na da matuƙar sauƙi fiye da action verb, stative verb da auxiliary verb. Domin shi ba ya canzawa, saboda canzawar lokaci ko duba da mai aiki. Sauran verb ɗin su kan canza dalilin mai aiki ko shuɗewar lokaci. Would ba haka ya ke ba. Domin shi a duk lokacin da ya zo, ya kan zo a yadda ya ke ko yaushe a ko ina. Bari mu ga wannan taƙaitattun misalan.

AFFIRMATIVE

    1. I would go
    2. You would go
    3. He would go
    4. She would go
    5. It would go
    6. They would go
    7. We would go

Idan za a canza wani verb daga positive zuwa negative, kawai kalmar do not ake rubutawa a tsakanin subject da verb ɗin. Misali, daga: I play the violin. Zuwa: I don't play the violin. To idan za a canza modals zuwa negative, kalmar not ɗin kaɗai ake ƙarawa a gaban modal verb ɗin. Wato daga He would go zuwa He would not go kenan.

NEGATIVE

    1. I would not go
    2. You would not go
    3. He would not go
    4. She would not go
    5. It would not go
    6. They would not go
    7. We would not go

Idan kuma za a canza wata jimla zuwa tambaya, akan sa kalmar do ko does ne a farkon jimlar. Sannan kuma a canzawa subject da verb ɗin guri, sai a ƙara da alamar tambaya a ƙarshen jimlar. Misali, daga: I play the violin. Zuwa: Do I play the violin? Bawai do da does ne kaɗai ake aiki da su domin yin tambaya ba - akwai kalmomin WH. Kalmomin WH su ne what (me ye), when (yaushe), where (ina), which (wanne), who (waye), why (me ya sa) da kuma how (ya ya). Waɗannan kalmomin duk ana amfani da su kaman yadda ake aiki da do da does.

Su modals ba a saka kalmar do ko does a farkon jimla idan za a canza su zuwa tambaya. Modal verb É—in ake canzawa guri da subject É—in. Wato daga He would go zuwa Would he go?.

INTERROGATIVE

    1. Would I go?
    2. Would you go?
    3. Would he go?
    4. Would she go?
    5. Would it go?
    6. Would they go?
    7. Would we go?

Amma su modals a kan yi amfani da kalmomin WH tare da su domin yin tambaya. Kalmomin WH su ne what (me ye), when (yaushe), where (ina), which (wanne), who (waye), why (me ya sa) da kuma how (ya ya). WaÉ—annan kalmomin duk ana amfani da su a farkon jimla ne idan za a yi tambaya.

KALMOMIN WH

    1. What would I do?
    2. When would you go?
    3. Where would he go?
    4. Why would she go?
    5. How would it go?
    6. Where would they go?
    7. When would we go?

Sannan shine bare infinitive ne ke biyo shi. Infinitive shine verb a asalin yadda ake kafin a sarrafa shi da wani lokaci ko mai aiki. Infinitive shine verb tare da preposition to. Misali, eat zai koma to eat.

INFINITIVEBARE INFINITIVE
to eateat
to buybuy
to kickkick
to eateat
to gogo
to seatseat
to playplay
to runrun
to drinkdrink
to drivedrive
to eateat

A LURA

  • Ba a cewa: I would to eat my lunch.
  • Sai dai a ce: I would eat my lunch.
  • Ba a cewa: I would to play football.
  • Sai dai a ce: I would play football.
  • Ba a cewa: I would to play the violin.
  • Sai dai a ce: I would play the violin.
  • Ba a cewa: I would to run for 5km.
  • Sai dai a ce: I would run for 5km.

WaÉ—annan hanyoyi su ne ake bi wajen sarrafa wannan kalma, bari kuma mu duba hanyoyi da ake aiki da shi.

HANYOYIN DA AKE AMFANI DA WOULD

    1. Reporting will
    2. Past habit
    3. Hypothetical situation
    4. To need to
    5. Requesting

REPORTING WILL

ÆŠaya daga cikin ma'anonin would, shine aiki a matsayin past tense É—in will. Wato idan ka na bayar da labarin wani abu da ya faru a baya, duk inda kalmar will take, cireta ake a maye gurbinta da would. Misali, daga: I will go, zuwa: I would go.

Aliyu, ya ce: I will travel to Sokoto. Idan ka na bayar da labarin sai ka cire will É—in ka sanya would agurin. Daga nan zai koma, I would travel to Sokoto.

Misali:

  • I will visit you.
  • I would visit you.
  • Zan ziyarceka.
  • I will give you some money.
  • I would give you some money.
  • Zan baka wasu kuÉ—ade.
  • I will sell my phone.
  • I would sell my phone.
  • Zan siyar da wayata.
  • He will play the ukulele later.
  • He would play the ukulele later.
  • Zai kaÉ—a ukulele nan gaba.
  • They will visit us.
  • They would visit us.
  • Za su ziyartar mu.

PAST HABIT

Ana amfani da would domin nuna wasu ayyuka da mutum kan yi a wani lokaci a baya. Ma'ana wani aiki da ada can baya, kafin yanzu ya kan yi. Kaman ka ce, lokacin da nake É—an makaranta na kan je makaranta a makare. Ka ga wannan wani aiki ne da kake yi can baya, kafin yanzu.

Misali:

  • When I was teenager, I would play football.
  • Lokacin ina Æ™arami na kan yi wasan Æ™wallon Æ™afa.
  • When we were students, we would go to school lately.
  • Lokacin muna É—alibai mu kan je makaranta a makare.
  • When she kid, she would cry for 30 minutes.
  • Lokacin tana Æ™arama takanyi kukan minti 30.
  • When they are in Kano, they would not go to school.
  • Lokacin da suke Kano ba sa zuwa makaranta.
  • When you are 18, you would swim all day.
  • Lokacin ka na É—an shekara 18 ka kan wuni ka na iyo.

HYPOTHETICAL SITUATION

Hypothetical situation shine abun da bai faru ba a zahiri, sa a ce da a ce kaza-kaza ya faru da na yi kaza-kaza. Hypothetical situation da Hausa shine da a ce kaza kaza da kaza kaza.

Misali:

  • If I live in Katsina, I would visit Funtua.
  • Idan da a Katsina na ke da sai na zuyarci Funtua.
  • If we are richmen, we would travel to London.
  • Idan da mu masu kuÉ—i ne, da sai mun je London.
  • If they come early, they would have breakfast with us.
  • Idan da sun zo da wuri da mun ci abin safe tare da su.
  • If we work hard, we would succeed.
  • Idan mu ka yi aiki sosai, za mu yi nasara.
  • Za mu tsaya a nan. Mun gode.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.