Mai karatu barka da sake ganinka a wannan shafin cikin sabon darasi mai taken mene ne adverb. Wannan darasi na ɗauke da bayanai game da adverb tare da misalai domin mai karatu. Adverb dai wani ɓangare ne mai matuƙar mahimmanci ga kowane ɗalibi mai son koya ko inganta turancinsa. Kafin mu fara darasin, ga jadawalin darasin. Wato jerin abubuwan da za mu koyar a darasin.
1. Adverb
2. Adverb of degree
3. Adverb of frequency
4. Adverb of manner
5. Adverb of place
6. Adverb of time
1. Adverb
Adverb na nufin bayyanau da Hausa. Adverb wasu kalmomi da ake amfani da su domin su nuna yanayi, hali, wurin da aka aikata wani aiki ko wasu ayyuka. Adverb ɓangarene mai amfani ne sosai wajen fahimtar sassan magana, wanda shi kuma sashene na mai matuƙar mahimmanci a nahawun turanci.
Misali:
I always go to work lately.
Na kan je aiki a makare kullum.
He plays the violin every day.
Ya kan kaÉ—a goge kowace rana.
She often cooks rice and beans.
Ta kan girka shinkafa da wake.
You rarely read books.
Ba kasafai ka ke karanta littattafai ba.
We simply solved the problems.
Cikin sauƙi mu ka warware matsalolin.
They attend his birthday annually.
Su kan halarci bikin zagayowar ranar haihuwarsa duk shekara.
A misali na farko, kalmar always ta na nuna cewa kullum a makare na kan je aiki. Wato ta na ƙarin haske game da lokacin da nake zuwa aiki.
A misali na biyu kuma, kalmar every day ta nuna cewa kowace rana ya kan kaÉ—a goge. Wato kalmar ta nuna lokaci da kuma maimaituwar aikin kaÉ—a goge da ya kan yi.
A misali na uku ma kalmar often ta nuna cewa ta kan girka shinkafa da wake sosai. Wato kalmar often ta nuna cewa ta na son girka shinkafa da wake kai a kai.
A misali na huÉ—u ma kalmar rarely ta nuna cewa ba kacika karanta littattafai ba. Wato karanta littafi ba dabi'arka ba ce.
A misali na biyar kuma kalmar simply ta nuna cewa sun warware matsalolin cikin sauƙi. Kalmar simply ta nuna cewa a cikin sauƙi ba tare da wata wahala suka warware ta ba.
Sai misali na shida kuma na karshe, kalmar annually ta nuna cewa duk shekara su kan halarci bikin zagayowar ranar haihuwar abokinsu.
WaÉ—annan kalmomin always, every day, often, rarely, simply da kuma annually sune adverb. Domin su ke nuna lokaci, yanayi, hali, guri ko muhallin da aka yi ayyukan gaba É—aya. Ga bayanan sassan adverb É—aya bayan É—aya kuma filla-filla.
2. Adverb of degree
Adverb of degree na nuna yanayi, hali ko tsananin da mutum ya yi wani aiki ko wasu ayyuka.
Ga kaÉ—an daga cikin kalmomin da ke rukunin adverb of degree:
Almost - kusan gaba É—aya
Bodly - a jarumce
Hardly - a wahalce
Just - kawai, hakan nan
Roughly - a kausashe
Simply - a sauƙaƙe
Misali:
I roughly respond to his questions.
A kausashe na amsa masa tambayoyinsa.
He bodly fight against smoking.
A jarumce ya ke faÉ—a da shaye shaye.
She hardly speaks English.
Ta na shan wahalar yin turanci.
You simple get along with her.
A sauƙaƙe ka shawo kanta.
We have just arrived in London.
Yanzun nan muka iso birnin landan.
3. Adverb of frequency
Adverb of frequency kalmomine da suke nuna maimaituwar wani aiki.
Ga kaÉ—an daga cikin kalmomin da ke rukunin adverb of frequency:
Always - kullum
Occasionally - lokaci-lokaci
Often - kai a kai
Rarely - ba kasafai ba
Usually - yadda aka saba
Misali:
They always play tennis after school.
Su kan yi wasan tennis bayan tashi a makaranta.
I occasionally play the ukulele.
Jifa-jifa na kan kaÉ—a ukulele.
He often plays the harmonica.
Ya kan yawaita busa madujala.
She rarely sings at a party.
Ba ta cika yin waƙa a wajen taro ba.
4. Adverb of manner
Adverb of manner kuma kalmomine da ke nuna hali ko yanayin da mutum ya ke wani aiki ko wasu ayyuka.
Ga kaÉ—an daga cikin kalmomin da ke rukunin adverb of manner:
Beautifully - a kyautace
Calmly - a cikin nutsuwa
Carefully - a nitse
Generously - a mutumce
Happily - a farin ciki
Neatly - a tsaftace
Patiently - a haƙurce
Softly - a tausace
Quickly - a gaggauce
Well - da kyau, a kyautace
Misali:
He calmly explain the lesson.
Cikin kwanciyar hankali ya ke jawabin darasin.
She is patiently waiting for him.
Ta na jiransa cikin haƙuri (ko a haƙurce).
You quickly wrote that e-mail.
A gaggauce ka rubuta saƙon wancan e-mail ɗin.
They neatly fixed the computer.
A nutse su ka gyara na'ura mai ƙwaƙwalwar.
5. Adverb of place
Adverb of place kuma kalmomi da ke bayar da bayanin wajen da aka yi wani aiki ko wasu ayyuka.
Ga kaÉ—an daga cikin kalmomin da ke rukunin adverb of place:
Above - a sama da, a saman
Below - a ƙasa da, a ƙasan
Everywhere - ko ina
Here - a nan, nan
In - ciki, cikin
Inside - a ciki, a cikin
Into - zuwa cikin
Nowhere - ba a ko ina ba
Out - waje
Outside - a waje
There - a can, can
Misali:
The banner above the door say exit.
Banar dake saman kofar an rubuta wajen fita.
The fishes live below the rivers.
Kifaye daban na rayuwa a cikin koguna.
I go nowhere.
Babu inda zanje.
I don't eat outside.
Ba na cikin abinci a waje.
She eats inside.
Ta kan ci abinci a cikin gida.
6. Adverb of time
Adverb of time kalmomine da ke nuna lokacin da aka yi wani aiki ko wasu ayyuka.
Ga kaÉ—an daga cikin kalmomin da ke rukunin adverb of place:
Annually - duk shekara
Daily - duk rana
Lately - a makare
Monthly - duk wata
Recently - a baya bayan nan
Today - yau
Tonight - yau da dare
Tomorrow - gobe
Weekly - duk sati, duk mako
Yearly - duk shekara
Yesterday - jiya
Misali:
Students gratuade annually.
ÆŠalibai kan kammala karatu duk shekara.
Salaries are paid monthly.
Akan bayar da albashi duk wata.
She is going to cinema tonight.
Yau da dare za ta je silima.
I met them yesterday.
Jiya na haÉ—u da su.
Da fatan ana biye da shafin nan. Mun gode