Mene ne Articles?

 


Mene ne Articles?

Articles wasu kalmomi ne da ake amfani da su tare da suna. Waɗannan kalmomi, kalmomi ne da ke bayar da ƙarin haske game da sunan da su ka zo tare. Articles sune a, an da kuma the. Akan rubuta su ne kafin sunan da suke bayar da haske game da shi.

 

Kalmar a ana amfani da ita tare da sunan da ya fara da furuci ko sautin harafin baƙi kaɗai.


Misali:

a boy - wani yaro

a car - wata mota

a cat - wata mage

a dog - wani kare

a man - wani mutum


Sai kuma an ana amfani da ita tare da sunan da ya fara da sauti ko furucin harafin wasali kaÉ—ai.


Misali:

an aeroplane - wani jirgin sama

an egg - wani ƙwai

an orange - wani lemu

an owl - wata mujiya

an umbrella - wata lema 


Kalmar the kuma ana amfani da ita kafin sunan da ya fara da sauti ko harafin baƙi ko wasali.


Misali:

the apple - tufar

the drum - gangar

the cake - kek É—in

the axe - gatarin

the gun - bindigar


INDEFINITE ARTICLE

Indefinite articles sune a da an. Waɗannan kalmomin ma'anarsu daya. Sai dai wajen da ake aiki da su ya ɗan bambanta. Kaman yadda bayani ya gabata a misalai da ke sama - idan suna ya fara da sauti ko harafin baƙi ana amfani da a, idan kuma suna da sauti ko harafin wasali ya fara sai a yi amfani da an.


Misali:

a dog - wani kare

a car - wata mota

a cat - wata mage

an apple - wata tufa

an egg - wani ƙwai

an owl - wata mujiya


A lura a da an ba ruwansu da jinsi, a cat (wata mage), a dog (wani kare), an orange (wani lemu) da kuma an ice (wata ƙanƙara). Domin ta na iya kasancewa wani ya yi tunanin cewa ana amfani da a kafin sunan dake jinsin maza, shi kuma an kafin sunan dake jinsin mata. Idan ma mai karatu ya yi tunanin haka, to ba haka abun yake ba.


Ana amfani da a ko an a cikin magana lokacin da za a ambaci sunan wani abu a karon farko, ko sunan da wanda ka ke magana da shi bai san shiba, ko kuma sunan abun da ba a sani ba.


Misali:

A boy wants to see you.

wani yaro na son ganinka.


A girl is skipping.

wata yarinya ta na wasan igiya.


I saw an axe beside my hut.

na ga wani gatari a gefen bukkata.


I ate an apple last night.

Na ci wani apple daren jiya.


An unknown person steals a car.

Wani da ba a sani ba ya saci wata mota.


DEFINITE ARTICLE

Kalmar definite article ita ce the. Ana amfani da ita kafin suna domin nuna cewa wannan sunan kafin yanzu wato a baya an ambace shi, ko kuma an san shi. Saɓanin indefinite articles waɗanda sun kasance ana amfani da su tare da sunan da aka jahilta.


Misali:

The boy who wants to see you is your brother.

yaron da ke son ganinka ƙaninkane.


The girl who is skipping is my neighbour.

yarinyar da ke wasan igiya maƙwabciya ta ce.


The axe I saw belongs to the woodcutter.

gatarin da na gani ta mai faskarece.


The car which was stolen is yours.

Motar da aka sace takuce.


GWAJIN FAHIMTA:

Cike guraben da aka bari a sunayen da ke tafe.

(a/an) a cup 

(a/an) a chair

(a/an) an apple

(a/an) an orange

(a/an) _ avocado

(a/an) _ umbrella

(a/an) _ aeroplane

(a/an) _ spacecraft

(a/an) _ ambulance

(a/an) _ pomegranate


ABIN LURA

Akwai wasu kalmomi da kan zo da wata dabi'a. Duk da cewa su baƙaƙene amma akan furtasu da sautin wasali. Misali, kalmar X-ray duk da ta fara da baƙi, amma wannan baƙi da sautin wasali ake furtashi. An x-ray ake cewa ba a x-ray ba.


Hakama akwai wasali da kan zo da sautin baƙi. Misali, wasalin 'U' a kalmomin university da unicorn da 'U' a kalmomin urban ko umbrella ba furucinsu ɗaya ba.


A unicorn - ingarman doki 

A university - wata jami'a

An uncle - wani kawu

An umbrella - wata lema


Haka ma harafin H duk da cewa baƙine, amma wani lokaci idan ya zo a farkon kalma ba a furtashi, sai dai a fara karanta wannan kalma daga harafin da ya zo bayansa. Misali, harafin H a kalmar hour da kalmar honey ba ɗaya bane.


A honey - wata zuma

A house - wani gida

An hour - wata sava


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.