Mene ne IDIOM?

 


Mai karatu mu na yi ma barka da sake kasancewa da shafin nan. Mu na fatan dai ana jin daɗin kasancewa da mu. Sannan kuma mu na fatan darussanmu na amfanarku. A yau mun zo da wani ɓangare mai matuƙar mahimmanci da ya kamata duk wani mai ƙoƙarin koyan turanci ya ɗan san shi. Wannan ɓangare ko mataki dai shine IDIOM. Mene ne shi da kuma misalansa duk su na tafe a darasin nan.


Kafin mu fara bayani bari mu kawo wasu misalai taƙaitattu domin yin matashiya ga mai karatu.


1. A wolf in sheep's clothing

2. The dark horses

3. To hit the sack.

4. Underdog.


1. A wolf in sheep's clothing

Wannan karin magana na nufin kura da fatar akuya. Wato ka na tsammanin wani zai taimakeka ko goyama baya, amma shi a zuciyarsa ba haka ba ne, domin cutar da kai yake so ya yi.


Misali:

At the end, I found the man's plan was a wolf in sheep's clothing.

Daga ƙarshe na gano cewa ashe shirin mutumin kurace da fatar akuya.


She understands that it is a wolf in sheep's clothing, that is why she does not give them anything.

Ta gano cewa al'amarin kurace da fatar akuya, shiyasa bata ba su komai ba.


2. The dark horses

Wannan karin magana na nufin wani mutum ko wata ƙungiya su yi abun da ba a zato ba a tsammaninsa.


Real Madrid is the dark horses of the UEFA Champions league of 2022.

Kungiyar Real Madrid ita ce ta yi abun da ba a zato ba a tsammaninsa a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai na shekarar 2022.


3. To hit the sack

Wannan karin magana na nufin mutum ya je ya yi bacci.


Misali:

I normally hit the sack at 9pm.

Na saba kwantawa bacci da ƙarfe 9 na dare.


She hits the sack lately and wakes up very early.

Ta kan kwanta a makare, kuma ta farka da sanyin safiya.


4. Underdog

Wannan karin magana na nufin wani mutum ko wata ƙungiya da ba a tsammanin za su taɓuka abun a zo a gani a wata gasa.


Misali:

F.C. Porto are the underdog in the tournament.

A gasar cin kofin ƙungiyar F.C. Porto ba zaton zata taɓuka abun a zo a gani.


The boxer is the underdog.

Ɗan damben zamanin ba a tsammanin zai taƙuka abun a zo a gani.


Mene ne IDIOM?

Idiom wata hanyace ta magana da ake aiki da ita a turanci wanda kuma ba a iya fahimtarta ta hanyar kalmomin da aka furta ko rubuta har sai an fassarawa mutum me ake nufi da wannan magana.


Idiom a taƙaice shine karin magana kaman yadda misalai su ka gabata a sama. Karin magana ba a iya fahimtar sa ta hanyar fassara kalmomi da ya ƙunsa face an fassarawa mutum.


Ga jerin wasu IDIOM É—in da za mu yi misalai a kan su

1. Clear as bell

Wannan karin magana na nufin wani abu mara wahalar fahimta. Wato abun da kowa zai iya fahimtarsa.


Misali:

The lesson is as clear as bell.

Darasin na sauƙin fahimta.


2. Cheapskate

Wannan karin magana ana amfani da shi domin nuna cewa wani mutum ba ya son kashe kuÉ—i.


Misali:

He is a cheapskate that why he cannot buy a new car.

Ba ya son kashe kuÉ—i shiyasa ba zai iya siyan mota ba.


3. A piece of cake

Wannan karin magana na nufin wani aiki mai sauki mara wahala.


Misali:

Our English exam was a piece of cake.

Jarabawar mu ta English na da sauƙi.


Learning Hausa on internet is not a piece of cake.

Koyan Hausa a intanet ba abune mai sauƙi ba.


It's a piece of cake for Bayern Munich to win its matches.

Abu ne mai sauƙi ga Bayern Munich ta yi nasara a wasanninta.


4. To catch someone red-handed

Wannan karin magana ana amfani da shi domin nuna cewa an kama wani dumu-dumu a yayin da ya ke aikata wani lefi.


Misali:

The police have caught the criminal red-handed.

'Yan sandan sun kama mai lefin a lokacin da ya ke aikata laifin.


His mother catches him red-handed with the sweet.

Mahaifiyarsa ta kama shi da alawar da ya sata.


The student was caught red-handed doing exam malpractice.

ÆŠalibar an kama ta ta na satar amsa.


To have a frog in ones throat

Wannan karin magana a na amfani da shi a lokacin da mutum baya iya magana sosai, saboda maƙoshinsa ya bude saboda rashin lafiya ko sanyi.


Misali:

5. I am not able to speak well, because I've a frog in my throat.

Ba zan iya magana sosai ba domin maÆ™oshina ya bushe 


6. Our professor can't deliver his lecture, because he's a frog in his throat since Monday.

Malaminnu ba zai iya gabatar da lakcarsaba saboda maƙoshinsa ya bushe.


7. She sang at the concert, she had a frog in her throat though.

Ta yi waka a bikin duk da cewa maƙoshinta ya bushe.


8. We usually have frogs in our throats in winters.

Yawanci a sanyi maƙoshinmu na bushewa.


Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.