Mai karatu sannun da zuwa. Barka da ganinka a wani sabon darasi da a cikinsa za mu yi bayanin wasu kalmomin turanci da ma'anoninsu a Hausa.
Bookworm
Mutum mai son karanta littafi. Wani kalmar na nufin wani mutum mai sha'awar yin karatu.
Misali:
I want to be a bookworm.
Ina son zama mai san karatu.
My friend is a bookworm, he is always reads novels.
Abokina mutum ne mai son karanta littattafai, ko yaushe za ka sameshi ya na karanta littattafai.
She is not a bookworm as her sister.
Ita ba mai son karatubace kamar yar uwarta.
Our teacher advises us to be bookworm.
Malamin kan shawarcemu da mu zama masu son karatu.
Their friend Aliyu is a bookworm.
Abokinsu Aliyu mutum ne mai son karatu.
Cobbler
Wannan kalmar na nufin mai gyaran takalma ko mai ɗinkin takalma. Cobbler shine sunan mutumin da ke yin sana'ar gyaran takalma (idan sun tsinke ko sun yage). Sannan cobbler na da ma'ana ɗaya da kalmomin shoemender da shoe repairer. Haka kuma ana iya mayen cobbler da su.
Misali:
The cobbler have polished my shoes.
My gyaran takalman ya goge mun takalma.
I will take my shoes to cobbler for vamp replacement.
Zan kai takalmana wajen mai gyaran takalma ya canzamun saman takalma.
Covenant
Wannan kalma na nufin alƙawari ko yarjejeniya. Wato wata yarjejeniyar da wasu ɓangarori su ka haɗu su ka yi a tsakaninsu.
Misali
The two opposition parties are going to sit for a covenant next year.
Ɓangarorin hamayya guda biyun za su haɗu su yi yarjejeniya shekara mai zuwa.
Both parties have to obey the agreements reach on the covenant.
Ɓangarorin ya kamata su kiyaye alƙawuran da aka yi a yarjejeniyar.
We should sit for covenant.
Ya kamata mu zauna taro tsakanin mu.
Disposable
Wannan kalmar na nufin wani abu da ake siya bayan an gama aiki da shi sai a jefar da shi.
Distinctive
Wannan kalma na nufin na daban ko na musamman. Wato wani mutum ko wani abu na musamman wanda ya bambanta da sauran.
Damfool
Wannan kalmar na nufin wani wawa ko sakarai ko hamago. Wato wani mutum ma shirmaci.
Exacerbate
Wannan kalmar na nufin sa wani abu ya yi tsanani wanda daman ya na cikin tsananin sa. Wato wani da yake cikin tsanani, sai aka ƙara sa ka shi ya tsananta fiye da yadda yake a baya.
Hot-headed
Wannan kalmar na nufin fusata.
Luddite
Mutumin da ya tsani sabbin fasahohi.
Miserable
Wannan kalmar na nufin baƙin ciki sosai, ɓacin rai.
Penitent
Wannan kalmar ta na nufin wani mutum dake cikin na dama da damuwa bayan abubuwan da ya aikata a baya.
Penny-pincher
Wannan kalmar ta na nufin wani mutum da baya son kashe kuɗi.
Petrified
Wannan kalmar na nufin tsananin tsoro da firgici.
Sleepwalker
Wannan kalmar ta na nufin mutumin da ke tafiya ya na gyangyaɗi ko bacci.
Surly
Wannan kalmar na nufin bacin rai ko fushi sosai.
Tear-jerker
Wannan kalmar na nufin wani wasan kwaikwayo ko littafi dake sa mutum yin kuka. Wato wata magana ko labari mai ɗauke da abun tausayi sosai da zai sa mutum ya yi kuka.
Misali:
Safara movie was a tear-jerker I watched.
Shirin fim ɗin safara shirine da na gani wanda ya sa na zubar da hawaye.
The novel titled as The Parentsless Baby is a tearjerker.
Littafin nan mai taken The Parentsless Baby kan sa mutum ya zubar da hawaye.
Uncouth
Wannan kalmar ta na nufin wani mutum mara haƙuri, wanda ba shi da daɗin mu'amala.
Misali:
I don't want to meet him because he is an uncouth.
Ba na san haɗuwa da shi domin shi mutum ne mara fitinanne.